|
Kabilar Hezhe wata karamar kabila ce mai dogon tarihi da ke a arewa maso gabashin kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 1990, yawan 'yan kabilar Hezhe ya kai 4245. Idan an kwatanta su da sauran 'yan kabilu na kasar Sin, za a iya cewa, kabilar Hezhe ita ce mafi kankanta a cikin duk kabilu na kasar Sin. A halin yanzu, yawancinsu suna zama ne a gundumar Tongjiang da ta Fuyuan da Raohe da ke a bakin koguna na lardin Heilongjiang, saura kadan suna zaune a gundumar Leideli, da ta Susutun da Jiamusi da kuma sauran wurare.
Tun can shekaru aru-aru, kakannin-kakannin 'yan kabilar Hezhe sun fara zama a wurare da ke gababon kogin Songhua da na Heilong da Wusuli a arewa maso gabashin kasar Sin. Aikin su da farauta manyan sana'o'i ne gare su. A lokacin zafi, sun kan yi kamun kifaye, a lokacin sanyi kuwa su kan yi farautar namun daji kamar su kura da barewa da sauransu.
A zamanin da, abinci da 'yan kabilar Hezhe ke ci yau da kullum su ne kifaye da nama. Kuma su kan yi amfani da fatun kifaye da na namun daji wajen dinke tufafi da jaka da hula da kyalen damara da sauran irinsu. Amma yanzu ba haka ba ne, zaman rayuwarsu ya riga ya sami manyan sauye-sauye. Abincinsu da tufafi sun tashi kusan daidai da na mu.
'Yan kabilar Hezhe suna bin tsarin auren namiji daya da mace daya, amma ba su auren zumunci a tsakaninsu. Bisa al'adarsu, iyayen budurwa su ne su kan zabi saurayi da 'yarsu za ta aura ta hanyar yin kokawa da harba kibau da kamun kifaye da yin farauta da sauran irinsu. Bayan da aka yi bikin baiko, sai ango ya kan sanya babbar riga mai launi iri daban dabam, amarya kuwa ta kan sanya riga da wando masu launin ja, kuma ta canja kitson kanta daga guda daya zuwa biyu. 'Yan kabilar Hezhe su kan shirya gagarumin bikin daura aure ne da asuba. Bayan bikin, ango da amarya za su ci taliya, abin da ake nufi shi ne soyayyar da ke tsakaninsu za ta dade, kuma za su ji dadin zamansu har shekara da shekaru.
'Yan kabilar Hezhe suna magana da harshensu, amma ba su da rubutu. Yanzu, yawancinsu suna jin Sinnanci wato harshen kabilar Han. 'Yan kabilar Hezhe suna sha'awar rera wakoki ainun, wadanda ke nuna yabo ga wurarensu masu ni'ima, da zaman alheri, da soyayya, da sauransu. Haka nan kuma suna da nasu tatsuniyoyi da almara da wasan kwaikwayo game da labarin yin aikin su da farauta, da zaman rayuwa, da dabbobi, da jarumai, da aljanu, da sauransu iri dabam daban.
A kan yi sanyi kwarai a wurare da 'yan kabilar Hezhe ke zaune. Idan wani ya sami damar zuwa wurarensu a yanayin sanyi, zai tarar da amalanke da karnuka ke ja. A yanzu ma, kusan duk iyalansu suna kiwon karnuka a gidajensu, don yin amfani da su wajen jan amalanke. Karnuka wadanda ke jan amalanke mai daukar kayayyakin kilo 150 zuwa 200 suna iya tafiya da sauri a kan kankara. An ce, a rana daya, karnukan da ke jan amalanke suna iya tafiya har kilomita 100. (Halilu)
|